Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ce ya fi son yin aiki tare da Joe Biden maimakon Donald Trump bayan zaben shugaban Amurka a watan Nuwamba.
Mista Putin ya kuma ce shugaba Biden ya fi zama gogaggen dan siyasa, fiye da wanda ya gada.
Sai dai ya ce Rasha za ta yi aiki da duk wanda jama’ar Amurkan suka aminta da shi.
Shugaba Putin ya fadi haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin wani dan jarida, RshaPavel Zarubin
Ya ce “ya fi kwarewa.Ya fi hangen nesa.Tsohon dan siyasane. Amma za mu yi aiki tare da duk shugaban da Amurka suka aminta da shi.
Mr Putin ya kuma yi watsi da batun shekarun Biden da kuma lafiyar kwakwalwarsa, yana mai cewa lafiya lau ya gansa a lokacin da suka hadu shekaru uku da suka gabata.
Joe Biden dai da Donald Trump dukkaninsu sun fukanci suka da kuma bincike kan lafiyar kwakwalwarsu da cancantarsu ta shugabanci.