Gwamnatin Biden ta buƙaci ƴan majalisar dokokin Amurka su bayar da damar ƙara taimakawa Ukraine da dala biliyan 20.
Za a yi amfani da mafi yawancin kuɗin ne a kan ayyukan taimakon soji.
Tun bayan da Rasha ta fara mamaye Ukraine, Amurka ta bai wa ƙasar fiye da dala biliyan 100 a matsayin tallafi.
Wani jami’in gwamnatin Amurka ya ce za a ci gaba da bayar da irin wannan tallafi idan har buƙatar hakan ta taso.
Ko da yake wasu ƴan majalisar daga jam’iyyar Republican sun ce za a soki matakin ci gaba da bayar da irin wannan taimako