Shugaba Biden na Amurka ya sanar da ƙarin tallafin soji da tsaro ga Ukraine da ya kai kusan dala biliyan biyu da rabi.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage mako ɗaya Mista Biden ya kammala wa’adin mulkinsa.
Sai dai ana nuna damuwa kan yiwuwar sabon shugaban Amurka Donald Trump ka iya rage tallafin ƙasar ga Ukraine.
Biden ya ce samar da tallafin ga Ukraine domin kare kai daga mamayar Rasha na ɗaya daga cikin muhimman abubuwa ga gwamnatinsa.
Ya ƙara da cewa tuni ma’aikatar tsaron Amurka ta fara ƙoƙarin kai wa Ukraine ɗin dubun-dubatar makaman atilare da rokoko da motoci masu sulke.