Amurka ta sanar da saboda mamayar da ta yi wa Ukraine da kuma mutuwar madugun adawar ƙasar, Alexei Navalny.
Takunkuman sun shafi mutanen da ke da hannu a tsare Navalny da kuma yaƙin da Rasha take, kamar yadda Shugaba Joe Biden ya sanar.
Za a sa takunkumin hana fitar da kaya kan kusan kamfanoni ko mutane 100.
Tarayyar Turai ta kuma sanar da wasu takunkuman da Rasha ta mayar da martani ta hanyar haramta wa jami’an Tarayyar Turai shiga ƙasarta.
Babu ƙarin bayani kan tasirin da takunkuman za su yi a kan tattalin arzikin Rasha.
Cikin wata sanarwa, Shugaba Biden ya ce takunkuman za su tabbatar shugaban Rasha Vladmir Putin ya ɗanɗana kuɗarsa saboda kama-karyar da yake a cikin gida da kuma fito na fiton dayake da ƙasashe.
Takunkuman na zuwa ne mako ɗaya tun mutuwar fuju’a da Navalny a wani kurkuku da ke yankin Arctic mai tsananin sanyi. Mista Biden ya ce babu tantama kan zargin shugaban na Rasha.
Suna kuma zuwa a jajiberin cika shekara biyu na mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
“Shekara biyu da ta gabata, ya yi ƙoƙarin ɓatar da Ukraine daga taswira. Idan Putin bai ɗanɗana kuɗarsa ba saboda mutuwarsa da ɓarnar da ya yi, zai ƙara ƙaimi ne,” in ji Mista Biden cikin wata sanarwa.
Tarayyar Turai ta sanar da sa takunkumi kan kusan kamfanoni da mutane ɗari biyu da ake zargin sun taimaka wa Rasha wajen samun makamai da kuma hannu a garkuwa da yaran Ukraine, wani abu da Rasha ta musanta.
A martaninta, ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta ce ta faɗaɗa jadawalin sunayen jami’an EU da ƴan siyasar da ta haramta wa shiga ƙasarta.