fidelitybank

Biden na son ganawa da Tinubu

Date:

Shugaban Amurka Joe Biden ya aike da gayyata ga shugaban Najeriya Bola Tinubu domin gudanar da wata tattaunawa tsakaninsu.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya, Ajuri Ngelale, ya fitar ya ce jakadan shugaban Amurka na musamman, kuma mataimakin sakataren harkokin wajen ƙasar, Ambasada Molly Phee, ne ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci shugaba Tinubu a fadarsa.

Mista Phee ya shaida wa Tinubu cewa shugaban Amurka Joe Biden na buƙatar ganawa ta musamman da shi, a lokacin babban taron Majalisar Dinkin Duniya da za a gudanar a birnin New York cikin watan Satumba.

Jakadan na Amurka ya ce, Tinubu ne kaɗai shugaban Afirka da shugaban Amurka ya karrama da gayyatar ganawa da shi.

Ya ƙara da cewa “Mun san akwai hanyoyin da za mu bi domin ƙarfafa zuba jarin Amurka a Najeriya, kuma muna son yin aiki kafaɗa-da-ƙafaɗa da kai domin cimma hakan, a wani ɓangare na inganta tattalin arzikin Najeriya da ma na Afirka”.

“Muna yabawa da irin ƙoƙarin da kake yi wajen samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari. Kan haka ne shugaba Joe Biden ke buƙatar ganawa da kai a lokacin babban taron Majalisar Dinkin Duniya, kuma kai kaɗai ne shugaban da ya buƙaci ganawa da kai daga Afirka. Wannan kuma alama ce da ke nuna cewa ya yarda da nagartar shugabancinka,” in ji jakandan na Amurka.

sun newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp