Shugabanni da manyan ‘yan siyasa na duniya na jinjina wa shugaban Amurka Joe Biden bayan yanke shawarar janyewa daga takarar shugaban kasa.
Shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, ya kira Mr Biden “abokin gaske ga al’ummar Yahudawa”, inda ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant ya rubuta a X cewa tsayin daka da goyon bayan da ya bayar a yakin da ake yi a Gaza ya kasance abun a yaba.
Firaiministan Australiya Anthony Albanese ya ce Mista Biden ya kasance “aboki na gaske ga Australia”.
Tun da farko, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya nuna jin dadinsa ga abin da ya kira goyon bayan da Mr Biden ke ba wa yakin da Ukraine ke yi da mamayar Rasha.
Ita kuwa fadar mulki ta Kremlin ta Rashar, cewa kawai ta yi, tana bibiyar lamarin.


