Sanatan Amurka kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Mitt Romney, ya yi kira ga Donald Trump da Joe Biden da su haƙura da takara a shekarar 2024 don bai wai sabbin ‘yan siyasa dama.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan shirinsa na yin ritaya.
Ya ce ya ɗauki matakin ƙin sake tsayawa takara a shekarar 2024 saboda lokaci ya yi da za a bai wa sabbin jini “damar zama shugabanni.”
Mista Romney, mai shekaru 76, ya shafe shekara 20 a harkokin siyasar Amurka, ciki har da gwamnan Massachusetts.
A cikin ‘yan shekarun nan, fitaccen ɗan jam’iyyar Republican ɗin ya zama mai sukar Biden da Trump.
Zai ci gaba da rike mukaminsa har zuwa ƙarshen wa’adinsa na majalisar dattawa a watan Janairun 2025.
A cikin wani bidiyo da Romney ke bayyana zaɓin nasa na ƙin sake tsayawa takara, wanda aka wallafa a shafukan sada zumunta a ranar Laraba da yamma, ya nuna cewa shekaru sun taka rawa wajen yanke shawararsa. In ji BBC.


