fidelitybank

BEPU ta nesanta kanta a kan kashe mutane biyu a Birnin Gwari

Date:

Ƙungiyar ci gaban al’ummar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna, BEPU ta ce ta damu ƙwarai tare da yin Allah-wadai kan kisan rubdugu da aka yi wa wasu mutum biyu da ake zargin makiyaya ne da ke da alaƙa da ƴan fashin daji.

Ƙungiyar ta BEPU ta nesantar da kanta da yadda aka kashe mutum biyun tare da gargaɗi kan cewa jama’a su daina ɗaukar doka a hannunsu idan ransu ya ɓaci inda ta buƙaci jama’a su rinƙa kai kokensu ga hukumomin da suka dace.

Haka kuma BEPU ta jinjina wa jami’an tsaro da ke ƙoƙarin tabbatar da tsaro a yankin na Birnin Gwari amma duk da haka ta nuna rashin jin daɗinta kan yadda ake bayar da rahotanni marasa daɗi kan Birnin Gwari inda ta ce wasu rahotannin za su iya jefa mazauna ƙaramar hukumar cikin hatsari.

BEPU ta ce gwamnati ta yi gaggawa wurin fitar da sanarwa ba tare da zurfafa bincike ba kan mutanen da aka kashe inda ta ce mutanen da ake zargin makiyaya ne ba makiyaya bane.

Ƙungiyar ta ce bisa bincikenta, waɗanda aka kashen da ake zargin makiyaya ne ba ma ƴan Najeriya bane inda ta ce masu ayyukan ta’addanci ne da suka zo daga Sudan waɗanda kuma suna daga cikin masu kai hare-hare a yankin na Birnin Gwari.

national tribune newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp