Dan wasan Faransa, Karim Benzema, ba zai buga gasar cin kofin duniya ta 2022 ba, bayan da ya samu rauni a cinyarsa ta hagu yayin atisaye ranar Asabar a Doha.
Binciken MRI ya tabbatar da cewa kyaftin din Real Madrid ya samu tsagewar tsoka kuma zai yi jinyar makonni uku.
Gasar cin kofin duniya ta 2022 da za a yi a Qatar yanzu za ta kasance na farko tun 1978 da ba za a buga wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or na yanzu ba.
“Ban taba kasala a rayuwata ba amma a daren yau dole ne in yi tunanin kungiyar, kamar yadda na saba yi.
“Don haka dalili ya ce in ba da wuri na ga wanda zai iya taimaka wa ‘yan wasanmu su samu gagarumin gasar cin kofin duniya,” Benzema ya rubuta a Instagram.h
A ranar Talata ne Faransa za ta fara kare kofin da ta lashe shekaru hudu da suka gabata a kan Australia.
Kamar yadda dokokin FIFA suka tsara, Les Bleus na da awanni 24 kafin wasansu na farko don tabbatar da wanda zai maye gurbin Benzema a cikin tawagar.
Kylian Mbappe, Antoine Griezmann, Olivier Giroud, Marcus Thuram da Ousmane Dembele su ne sauran ‘yan wasan gaba da suka rage a tawagar Faransa.