Gwamnan jihar Benue, Rabaran Fr. Hyacinth Alia, ya kaddamar da kwamitocin kwato kadarori guda biyu domin kwato kadarori na gwamnatin jihar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Tersoo Kula ya fitar ranar Lahadi, ta ce daya daga cikin kwamitocin na aiki ne a matakin jiha yayin da daya a matakin kananan hukumomi.
Sanarwar ta kara da cewa, “Kwamitocin, da dai sauransu, an ba su damar tantance dukkan kadarorin gwamnati da suka hada da filaye, motoci, gidaje, daki da sauran injuna”.
Dukkan kwamitocin biyu za su sami wakilai daga;
1. Ma’aikatar Tsaro ta Jiha
2. Yan Sanda
3. Sojoji
4. Jami’an Civil Defence na Najeriya.