Gwamnatin jihar Benue ta ƙaddamar da wata rundunar tsaro ta ‘yan sa-kai mai suna Volunteer Guards.
Benue na daya daga cikin jihohin da ake samun rikicin manoma da makiyaya, abin da kan kai ga kashe-kashe.
Daga cikin ayyukan ‘yan rundunar wadanda aka danka wa makamai, za su haɗu da ƴan sandan Najeriya da wasu hukumomin tsaro don mayar da martani kan hare-haren.
Saboda ƙaruwar hare-hare da garkuwa da mutane a ƙasar, kananan hukumomi na tashi tsaye domin kare kansu da al’ummarsu.
Ko a baya ma gwamnatin jihar Zamfara ta arewa maso yamma ta bukaci al’ummarta da su mallaki makamai domin kare kansu daga ƴan ta’adda da barayin daji.
Wadanda suka addabe su da miyagun hare-hare da rashin kwanciyar hankali na gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.
Jihohin yankin Kudu maso Yamma da Kudu maso gabashi, suma sun haɗa irin wannan rundunar tsaro mai suna Amotekun da Ebube-Agu don taimakawa wajen tsaro.
Masana na ganin jihohi sun dawo daga rakiyar hukumomin tsaro na kasar ne, shi ya sa suke samar da rundunonin tsaro na kansu. In ji BBC.
Domin maganin matsalar tsaro ta masu garkuwa da mutane da masu tsattsauran ra’ayi da ke ta kara habaka.


