Gwamnatocin jihohi uku na cikin shirin ko-ta -kwana, sakamakon ƙaruwar fargabar samun ambaliya saboda yiyuwar sakin ruwan madatsar Lagdo ta Kamaru.
Jihohin sun haɗar da Benue da Edo da kuma jihar Bayelsa, waɗanda tuni suka fara shiri don kauce wa barazanar ambaliyar, kamar yadda Jaridar Punch a ƙasar ta ruwaito.
Kodayake ma’aikatar albarkatun ruwa ta Najeriya ta yi watsi da rahotonnin da ke cewa an buɗe madatsar ruwan, tuni jihohin suka fara shirya wa barazanar.
Gwamnatin jihar Benue ta ce ta fara aikin wayar da kan jama’a sakamakon ƙaruwar saukar ruwan sama da ake samu a ƴan kwanakin nan.
Jami’ar yaɗa labarai na hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar, Tema Ager ta ce gwanatin jihar na jiran umarni daga ma’aikatar albarkatun ruwa ta ƙasar.