Dan wasan tsakiya na Real Madrid, Jude Bellingham, ya kamo tsohon dan wasan kungiyar Cristiano Ronaldo, yayin da ya kafa tarihi na musamman bayan fara wasa a Los Blancos.
Bellingham, wanda ya koma Real Madrid a wannan bazarar daga Borussia Dortmund, yana taka rawar gani a gasar La Liga, inda ya yi koyi da yadda Ronaldo ya fara buga wasa a kungiyar.
Ya buga wasansa na farko na Real Madrid ne da kwallo a ragar Athletic Bilbao a gasar La Liga a makon jiya.
Bellingham ya kuma zura kwallaye biyu tare da bayar da taimako a wasansa na gaba a gasar La Liga da Real Madrid ta yi a ranar Asabar inda ta doke Almeria da ci 3-1.
Wannan farawar mai ban mamaki na nufin dan wasan mai shekaru 20 ya zura kwallaye uku da taimakawa a wasanni biyu na farko na gasar La Liga.
Abu ne da ya sanya Bellingham cikin babban tarhi, domin karo na karshe da dan wasa ya fara taka rawar gani a Real Madrid shi ne Ronaldo a shekarar 2009, in ji BBC.
Ronaldo ya koma Real Madrid ne daga Manchester United a shekara ta 2009 kuma ya zura kwallo a ragar Deportivo La Coruña a wasansa na farko. Kyaftin din na Portugal ya ci gaba da burgewa da kwallaye a ragar Espanyol, Xerez, da Villarreal, inda ya zura kwallaye a wasanni hudu na farko da ya kafa.