fidelitybank

Bellingham ne a kan gaba wajen cin kwallaye a Laliga

Date:

Real Madrid ta lashe dukkan wasa uku da ta buga tun bayan fara La Liga a kakar nan, ciki har da wanda ta je ta doke Celta Vigo 1-0 ranar Juma’a 25 ga watan Agusta.

Sabon dan wasan da Real ta dauka a bana Jude Bellingham ne ya ci mata kwallo sauran minti tara a tashi daga karawar.

Kawo yanzu dan wasan tawagar Ingila ya zura kwallo hudu a raga a wasa uku da ya buga wa Real Madrid karawa uku da fara babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Real ta fara wasa da bude La Liga da cin Bilbao 2-0 ranar 12 ga watan Agusta, inda Rodrygo ya fara cin kwallo, sannan Jude Bellingham ya kara na biyu.

Ranar 19 ga watan Agusta Real Madrid ta je ta doke Almeria 3-1 a wasan mako na biyu a La Liga.

Almeria ce ta fara cin Real Madrid a minti uku da take leda ta hannun Sergio Arribas, sai dai minti 16 Bellighma ya farke kwallo.

Bayan da suka koma hutu a zagaye na biyu ne Real ta kara na biyu ta hannun Bellingham, sannan Vinicius Junior ya kara na uku.

Bellingham, wanda ya zura kwallo hudu daga karawa uku a La Liga ya koma Real Madrid daga Borussia Dortmund kan fam miliyan 88.5.

Ranar Asabar Real Madrid za ta karbi bakuncin Getafe ranar 2 ga watan Satumba a wasan fafatawar mako na hudu. In ji BBC.

Sakamakon wasannin La Liga uku da Real Madrid ta buga a bana:

Asabar 12 ga watan Agusta 2023

  • Ath Bilbao 0 – 2 Real Madrid

Asabar 19 ga watan Agusta 2023

  • Almeria 1 – 3 Real Madrid

Juma’a 25 ga watan Agusta 2023

  • Celta Vigo 0 – 1 Real Madrid

nnn.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp