Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Mohamed Bazoum ranar Laraba 26 ga watan Yulin 2023, an ga hamɓararren shugaban tare da Mahamat Idris Deby, shugaban Chadi.
Mahamat Deby ya je Niamey ne a ƙoƙarinsa na shiga tsakanin masu juyin mulkin da kuma ƙungiyar raya tattalin arziƙin Afirka ta Yamma (Ecowas) wadda ta ba wa sojojin Nijar wa’adin kwana bakwai su mayar da Bazoum kan karagar mulki.
Dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa ne suka yi wa Bazoum juyin mulki tare da tsare shi a wani sashe na fadar shugaban ƙasar ta Nijar.
Tun daga ranar, ba a ga hamɓararren shugaban a bainar jama’a ba, don haka ba a san taƙamaimai halin da yake ciki ba.
Ƙasashen Yamma da ƙungiyoyin ƙasashe kamar Majalisar Ɗinkin Duniya da Ecowas da Amurka da Faransa har ma da Rasha sun yi ta kira ga sojojin da suka yi juyin mulki a kan su saki Bazoum tare da iyalansa.