Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya sake tabbatar da cewa gwamnatin mulkin sojan da ta tsige shugaban Nijar Mohamed Bazoum daga kan karagar mulki ba ta da hurumin ba da umurnin janyewar sojojin Faransa daga yankin Sahel na Nijar.
Macron na mayar da martani ne ga sanarwar da gwamnatin mulkin sojan kasar ta yi a ranar 9 ga watan Satumba inda suka zargi Faransa da yin amfani da dabaru na yaudara tare da haddasa tsaiko wajen janye sojojinta 1,500 kamar yadda wani shafin yada labarai mai zaman kansa ActuNiger ya ruwaito.
“Muna cikin Nijar ne domin yakar ta’addanci, bisa bukatar ƙasar da hukumominta da aka zaba, wadanda suka hada da shugaba Bazoum, da gwamnatinsa da majalisar dokokin kasar,” in ji Macron yayin taron G-20 a Indiya.
Ya kuma jaddada cewa, matakin da Faransa ta dauka ya taka muhimmiyar rawa wajen rage hare-haren ta’addanci a Nijar, duk kuwa da hasarar rayukan sojojin Faransa.
Macron ya kuma bayyana cewa, Faransa na haɗa kai da shugabannin kasashen yammacin Afirka domin ganin an sako Bazoum da kuma maido da tsarin mulkin Nijar.
Sabanin haka, shugaban mulkin sojan kasar Birgediya Janar Abdourahmane Tchiane ya zargi Faransa da goyon bayan shirin kungiyar Ecowas na shiga tsakani a Nijar tare da mayar Bazoum kan muƙaminsa.
Ban da haka kuma, wata kungiyar farar hula mai goyon bayan soji mai suna M62 ta shirya wani gagarumin raye-raye a Yamai domin nuna goyon bayansu ga shugabannin sojojin da kuma kiran janyewar sojojin Faransa.
Bikin ya samu halartar jami’an soji da dama wadanda suka godewa magoya bayansu bisa gagarumin taron da suke yi na yakar Faransa


