Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta NDLEA, ta ce, ta kama wata bazawara da ta yi niyyar zuwa Saudiyya da hodar ibilis a cikin wasu takalma a filin jirgin sama na Legas.
A wani saƙo da hukumar ta fitar a shafinta na Tuwita ta ce ta kuma ƙwace hodar ibilis da nauyinta ya kai kilogiram 5.6kg da wasu ƙwayoyin da aka yi niyyar safararsu zuwa ƙasashen Australiya da Cyprus a filin jirgin maƙare cikin wasu saiwoyin doya.
An kama bazawarar mai suna Ajisegiri Kehinde Sidika mai shekara 56 a filin jirgin saman birnin Legas a lokacin da take ƙoƙarin hawa jirgi zuwa Saudiyya da hodar ibilis da nauyinta ya kai giram 400 naɗe a cikin takalma.