Shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron, ya naɗa abokinsa mai matsakaicin ra’ayi, Francois Bayrou a matsayin sabon firaministan ƙasar.
A makon da ya gabata ne ya rusa tsohuwar gwamnatin da ya zaɓa bayan wata uku.
Ƙasar Faransa na cikin ta shiga ruɗanin siyasa tun bayan zaɓen da mista Macron ya kira a farkon watan nan, wanda ya samar da majalisar dokoki da babu jam’iyyar da ke da rinjaye.
Mista Bayrou shugaban jam’iyyar, Democratic Movement – zai fuskanci kaubale a koƙarinsa na janyo hankalin jam’iyyun da suka samu rarraubuwar kawuna a majalisar dokokin ƙasar domin shiga gwamnatin ƙasar.
Abu na farko da zai fara cin karo da shi, shi ne batun aiwatar da kasafin kuɗin ƙasar.