Bayern Munich ta sayi dan wasan baya na kasar Netherlands, Matthijs de Ligt daga Juventus kan kwantiragin shekaru biyar akan kudi Yuro miliyan 77 kwatankwacin Fam miliyan 65.6.
De Ligt ya koma Juventus ne daga Ajax kan kwantiragin shekaru biyar a watan Yulin 2019 kuma ya shafe kakar wasanni uku tare da zakarun Seria A sau 36.
Dan wasan mai shekaru 22 ya lashe kofin Seria A daya da Coppa Italia daya a wasanni 117 da ya buga a Turin.
“Na yi matukar farin ciki da zama dan wasa a wannan babban kulob,” in ji De Ligt.
“FC Bayern na daya daga cikin kungiyoyin da suka yi nasara a Jamus, daya daga cikin kungiyoyin da suka yi nasara a Turai da kuma a duniya.”
“Na ji godiya ta gaske daga mahukuntan wasanni, kociyan kungiyar da kuma hukumar tun da farko, wanda ya gamsar da ni. A kan haka, kulob ne mai hazaka mai tafiyar da harkokin wasanni da manyan buri.
“Na yi matukar farin ciki da cewa yanzu na shiga cikin labarin FC Bayern.”