Bayern Munich ta kammala ɗaukar Vincent Kompany a matakin sabon kociyanta kan ƙwantiragin kaka uku.
Ɗan Belgium mai shekara 38 ya maye gurbin Thomas Tuchel, bayan da ya bar Burnley zuwa Bundesliga, inda ƙungiyoyi suka kai ga cimma matsaya.
Kompany ya lashe Championship da Burnley a 2022-23, amma ƙungiyar ta faɗi daga Premier League a bana, bayan da ta kare ta 19 a kasan teburi.
Kompany, wanda ya yi ritaya daga taka leda a 2020 ya karɓi aikin horar da Burnley daga Anderlecht a 2022, wanda ya tsawaita yarjejeniyarsa a bara zuwa kaka biyar.