Bayern Munich ta amince za ta sayi dan kwallon Tottenham, Harry Kane kan fam miliyan 86.4.
Kane, mai shekara 30, yana da sauran kunshin kaka daya, wadda za ta kare a karshen wasannin bana, yanzu zabi na wajensa ko zai yadda ya bar Premier League zuwa buga Bundesliga.
Kane shi ne kan gaba a yawan ci wa Tottenham kwallaye a tarihi, mai 280 a raga a wasa 435.
Tun farko an yi ta alakanta Kane da Manchester United a bana, daga baya Bayern Munich ta sanar da cewar tana zawarcin dan kwallon.
Kane ya lashe takalmin zinare karo uku a matakin wanda ci kwallaye da yawa a kakar Premier League, wato, Premier League Golden Boot.
Kane, wanda ya fara buga wa Tottenham tamaula a 2012 ya zama kan gaba a cin kwallaye a Premier League a kakar 2015-16 da 2016-17 da kuma 2020-21.
Kyaftin din tawagar Ingila ya ci kwallo 213 a gasar Premier a wasa 320, saura 48 ya haura Alan Shearer, mai tarihin yawan cin kwallaye a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Kane – wanda shi ne kan gaba a yawan ci wa tawagar Ingila kwallaye mai 58 – bai taba daukar wani babban kofi a Tottenham ko a Ingila ba.
Ita kuwa Bayern Munich kan dauki kofuna a kowacce kakar tamaula a Jamus, tana kuma daukar wasu a Turai.
Bayern Munich – wadda a yanzu Thomas Tuchel ke jagoranta – ta dauki Bundesliga na 33 jimilla, kuma a kakar da ta wuce ne ta dauki kofi na 11 a jere.
Zakarun na Jamus na da kofin Zakarun Turai na Champions League shida da kuma German Cup.