Konrad Laimer ya koma Bayern Munich, kan yarjejeniyar da za ta ƙare a ranar 30 ga watan Yunin 2027.
Mai shekara 26, da ke taka leda daga tsakiya ya bar RB Leipzig, bayan da kwantiraginsa ta ƙare a ƙarshen kakar nan a ƙungiyar da ta lashe DFB Cup na bana.
Laimer ya fara tamaula a matashin ɗan kwallo a Red Bull Salzburg, wadda ya fara yi wa wasa cikin Satumbar 2014.
A can Salzburg, ya lashe kofin babbar gasar Austrian da wasu ƙarin kofi uku kafin daga baya ya koma Leipzig kafin a fara kakar 2017.
Laimer ya fara buga wa tawagar Austria tamaula a cikin Satumbar 2019, kawo yanzu ya yi mata karawa 26 da cin kwallo biyu a raga.