Kungiyar Kwallon Kafa ta Bayelsa United ,ta kammala daukar Sam Adekunle.
Adekunle ya koma kungiyar Restoration Boys daga kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Abeokuta Stormers kan kudin da ba a bayyana ba.
Dan wasan na tsakiya ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyu da kungiyar ta Yenagoa.
Adekunle ya jagoranci Stormers zuwa gasar cin kofin Super Eight na NNL a Asaba.
Ya zo ne a matsayin wanda zai maye gurbin Ebedibiri Endurance wanda ya tafi Rivers United a watan jiya.
Ya buga wasan sada zumunci da Bayelsa United da Akwa United da Enyimba.


