Ana kara samun sabbin bayanai game da harin nan da ‘yan bindiga suka kai a wata coci da ke jihar Ondo a Najeriya a ranar Lahadi, lamarin da ya janyo mutuwar mutane da dama.
Sabbin bayanan ‘yan sanda sun ce maharan sun yi ɓad-da-kama a matsayin masu ibada, da suka halarci cocin kamar kowa.
Sannan daga bisani suka fara tashin abubuwan fashewar da suke tare da su, yayin da wadanda ke waje suka buɗe wuta.
Har yanzu dai ba a san dalilin da ya sa suka kai harin a garin Owo da ke kudu maso yammacin ƙasar ba.
Haka kuma ‘yan sanda ba su bayyana adadin wadanda suka mutu a hukumance ba. In ji BBC.