A ranar Juma’a ne shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dawo Najeriya bayan halartar taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 da aka kammala a makon jiya.
A cikin makon da ya gabata, Ajuri Ngelale, mashawarcin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai, ya yi shiru kan inda Tinubu yake, wanda rahotanni suka ce ya bar birnin New York a ranar 22 ga watan Satumba.
Kusan mako guda ba a san inda Tinubu yake ba, har sai da ya dawo Najeriya a daren Juma’a, duk da cewa wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce ya taso ne daga birnin New York zuwa birnin Paris.
A taron UNGA da aka kammala kwanan nan, shugaban Najeriyar ya yi jawabi a zauren taron inda ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya da su hada kai da kasashen Afirka wajen tunkarar kalubalen da suke fuskanta.
Tinubu, a matsayinsa na shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ECOWAS, ya nemi taimako domin sake kafa mulkin dimokuradiyya ta hanyar da za ta magance kalubalen siyasa da tattalin arziki da kasar ke fuskanta, ciki har da masu tsattsauran ra’ayi da ke neman haddasa rashin zaman lafiya a yankin.
A kan haka, shugaban ya kuma gana da masu zuba jari a Amurka kan bukatar bunkasa zuba jari a Najeriya.
Ya gana da ‘yan Najeriya a Amurka, inda ya bukace su da su zama jakadu nagari a kasar.