fidelitybank

Bayan shekaru 40 da yin kisan kai yanzu haka ya shiga hannu

Date:

Hukumomin a Amurka sun kama mutumin da ake zargi da da aikata kisan kai bayan shekara 40 yana wasan ɓuya da jami’an tsaro.

‘Yan sanda sun ce ana zargin Donald Santini mai shekara 65 da amfani da sunayen ƙarya 13 domin kauce wa kamun jami’an tsaro bayan kashe wata mata mai shekara 33 a jihar Florida ta Amurka a shekarar 1984.

An kama shi ne a yayin da yake aiki a matsayin shugaban hukumar ruwa a wata unguwa a jihar California.

An dai tisa-ƙeyarsa zuwa jihar Florida domin fuskantar tuhuma kan zarge-zargen da ake yi masa. In ji BBC.

Ana zarginsa da kashe wata mata mai shekara 33 a lokacin. Hukumomin sun ce Mista Santini shi ne mutum na ƙarshe da aka gani da matar kafin a tsinci gawarta a ɗaure cikin wata hanyar ruwa.

Hukumomin sun ce ya gudu daga yankin bayan da aka zarge shi da kashe matar.

An yi ta nuna hotunansa a gidajen talbijin na ƙasar a matsayin mutumin da ake nema ruwa-a-jallo a shekarun 1990, da 2005, da kuma 2013.

naija news today legits

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp