Dan majalisar tarayya mai wakiltar Enugu ta Gabas, Chimaroke Nnamani ya fice daga jam’iyyar PDP.
Wannan dai na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da tsohon gwamnan na Enugu ya sha kaye a takarar sanata a hannun dan takarar jam’iyyar Labour, Kevin Chukwu
A cewar hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, dan takarar jam’iyyar LP ya samu nasarar lashe kujerar ne bayan ya samu kuri’u 69,136 inda ya doke Nnamani wanda ya samu kuri’u 48,701.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa an gudanar da zaben ne a ranar Asabar, biyo bayan kisan da aka yi wa tsohon dan jam’iyyar LP, Oyibo Chukwu, kwanaki kadan gabanin zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Da yake mayar da martani kan sakamakon zaben, Nnamani, a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Litinin da ta gabata, ya bayyana hakan ne bayan tattaunawa da mukarrabansa da wadanda suka zabe shi.
Ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar ne saboda rashin jituwa da shugabannin jam’iyyar PDP na kasa.
Nnamani ya kuma tabbatar da saninsa da zababben shugaban kasa Bola Tinubu tare da alkawarin ci gaba da hada kai da shi.