Shugaban ƙasa, Bola Tinubu na kan hanyarsa ta komawa Abuja, babban birnin ƙasar bayan kwashe sama da mako biyu a Legas, domin bikin babbar Sallah.
Mai magana da shugaban ƙasar ya wallafa a shafinsa na X cewa Tinubun yanzu haka na kan hanyar komawa Abuja.
Bayan hutun sallah, Tinubu ya ƙaddamar da wasu ayyuka a lokacin da yake Legas, ciki har da na katafaren aikin gina titin gaɓar teku mai tsawon kilomita 700 wanda ya tashi daga Legas zuwa Calabar.
Haka nan ya halarci bikin cikar ƙungiyar haɓɓaka tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka (Ecowas) shekara 50 da kafuwa.