A yau ne ake gudanar da zaman makoki a Jamhuriyar Check, bayan harin da aka kai ranar Alhamis a Jami’ar Prague.
Za a sassauta tutocin ƙasar a gine-ginen gwamnati, za kuma a yi shiru na minti ɗaya da tsakar rana.
Mutane goma sha huɗu ne wani ɗan bindiga ya harbe a jami’ar, wanda daga bisani shi ma ya kashe kansa.
Ana kuma zargin ɗan bindigar ya kashe mahaifinsa a ranar, da wasu mutane biyu a wani daji da ke kusa da Prague a makon da ya gabata.


