A ranar Litinin ne ‘yan wasan Manchester United sun dawo daukar horo da misalin karfe 9 na safe bayan da suka sha kashi a hannun Liverpool da ci 7-0.
An ce koci Erik ten Hag ya isa filin atisayen sa’o’i biyu kafin ‘yan wasan.
Majiyoyin United sun ce zai tattauna da ‘yan wasan Man United sakamakon rashin nasara mafi muni da kungiyar ta yi a shekaru 91 a Anfield.
An tambayi Ten Hag yayin taron manema labarai na bayan wasan ko ’yan wasan sun yi yunkurin bayyana ra’ayinsu, sai ya amsa da cewa: “A’a, ban ba su dama ba sai yanzu.
“Dole ne mu yi magana a kan hakan, na ba da ra’ayi na ne kawai kuma gobe za mu yi magana game da hakan. Na san wannan tawagar za ta sake farawa kuma dole ne mu koma baya kuma mun nuna a baya za mu iya. “