Gamayyar kungiyoyin farar hula a arewacin kasar nan, sun yi kira ga shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, da ya yi murabus ko kuma a kore shi bisa zargin cin hanci da rashawa.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, shugaban gamayyar kungiyoyin farar hula na Arewa, Adamu Aminu Musa, ya bayyana cewa murabus din Abdulrasheed Bawa a wannan lokaci abu ne mai tsafta domin ceto martabar Najeriya.
Sanarwar ta ce: “Shugaban zartarwa na hudu, Mista Bawa, ya kasance kan gaba wajen zarge-zargen cin hanci da rashawa tun ma kafin a nada shi a matsayin shugaban, wanda aka yi imanin cewa yana tattare da cece-kuce da rufa-rufa.
Sanarwar ta kara da cewa Bawa yana aiki ne kamar sarki, inda yake amfani da ofishinsa wajen tursasasa, muzgunawa, da kuma tilastawa mutane yin abin da ya nema, ciki har da bankuna, wasu hukumomin gwamnati, da ‘yan Najeriya da ba su da wani laifi, tare da goyon bayan ubangidansa, babban lauyan gwamnati.
Adamu Aminu ya kuma yi zargin cewa Bawa ya tilastawa shugaban NIMASA daukar nauyin ‘yan uwansa zuwa kasashen waje karatu a jami’ar Centurion of Technology and Management, Bhubaneswar, India.
Ya yi zargin cewa shugaban na EFCC ya tursasa hukumar ta NCC tare da tursasa wa kaninsa aiki yayin da shi da kansa ya dauki wani dan gidan sa aiki a ofishin EFCC na Legas.