fidelitybank

Baturen ‘yan sanda a Jigawa ya rasu a ofishin sa

Date:

Baturan ‘yan sanda reshen karamar hukumar Jahun a jihar Jigawa, SP Abubakar Musa, ya fadi ya mutu a ofishin sa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP. Lawan Shiisu Adamu ya tabbatar da rasuwar a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Asabar.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da daddare da misalin karfe 9:00 na dare a ofishin DPO na sashen Jahun bayan doguwar jinya.

A cewarsa, “SP. Abubakar Musa ya rasu jiya da misalin karfe 9:00 na dare a lokacin da yake rufe bakin aikinsa.”

Ya bayyana cewa an garzaya da marigayin zuwa babban asibitin Jahun da kuma babban asibitin Rashid Shekoni sannan aka kai shi asibitin koyarwa na Aminu Kano inda aka tabbatar da rasuwarsa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP. Emmanuel Ekot Effiom ya jajantawa iyalan mamacin da rundunar ‘yan sandan Najeriya.

national tribune newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp