Ministan yaɗa labarai da wayar da kai, Mohammed Idris, ya yi watsi da kiraye-kirayen da ake na shugaba Bola Tinubu ya yi murabus, inda ya ce yunƙuri ne na karkatar da hankalin mutane.
A makon da ya gabata ne wasu gwamnoni daga jam’iyyar PDP, babbar jam’iyyar adawa a Najeriya suka buƙaci shugaba Tinubu ya ajiye muƙaminsa idan ba zai iya warware ƙalubalen tattalin arzikin da ƙasar ke fama da shi ba.
A ranar Lahadi ne, Idris ya ce shugaba Tinubu ba zai ajiye aiki ba kuma yana da ƙwarewar magance taɓarɓarewar tattalin arziki.
Cikin wata sanarwa, ministan ya ce matsalolin tattalin arzikin da Najeriya ke fuskanta ba su fi ƙarfin shugaba Tinubu ba kuma ba zai ajiye muƙaminsa ba.
“Zai ci gaba da dagewa wajen yaƙar matsalolin har a samu galaba a kan su, shimfiɗa tubalin sabuwar Najeriyar da ke tasowa.”
Najeriya dai na fama da taɓarɓarewar tattalin arziki mafi muni cikin shekaru, inda darajar kuɗin ƙasar ke ƙara faɗuwa kuma jama’a da dama na fama wajen samun abin kai wa bakin salati.


