Wata kotu a Kano ta aike da Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda, daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC zuwa gidan ajiya da gyaran hali.
Dan Bilki zai ci gaba da zama a gidan ajiya da gyaran hali, har zuwa 15 ga watan Maris.
Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da Dan Bilki Kwamanda ne daya daga cikin makusanta ga shugaba, Muhammadu Buhari gaban kotun Majistere da ke Nomansland bisa zargin bacin suna da tunzura al’umma.
A na tuhumarsa da batawa gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje suna, kan zargin cewar, gwamnan na Kano ya bayar da cin hanci kafin aka bai wa Shugaban Jam’iyyar APC Abdullahi Abbas takardar sheda ta zama shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano.