Mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin sadarwa na zamani, Bashir Ahmad, ya yi tsokaci kan gwamnan jihar Kano na gaba.
Ahmad ya bayyana cewa mataimakin gwamnan jihar a halin yanzu, Nasiru Gawuna yana da kwarewar jagorantar jihar Kano.
Ya yi nuni da cewa Gawuna na da ikon yin tasiri mai kyau kuma mai dorewa ga al’ummar jihar.
Karanta Wannan:Â Ba zan amince da tayin Tinubu ba – Peter Obi
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter, mai taimaka wa shugaban kasar ya bayyana Gawuna a matsayin kwararre mai kula da harkokin gudanarwa.
Ya rubuta: “Babu shakka Nasiru Gawuna kwararre ne mai gudanar da mulki, wanda ya kware a aikin gwamnati da kuma fahimtar kalubalen da Kano ke fuskanta a yau.
“Ina da cikakken kwarin gwiwa kan iyawar Dokta Gawuna na jagorantar Jihar mu zuwa ga kyakkyawar makoma.
“A matsayinsa na Gwamna zai yi tasiri mai dorewa a rayuwar Kanawa.”