An ceto Basaraken gargajiya mai daraja ta daya a Jihar Filato, Agwom Izere, Mai Martaba Dokta Isaac Azi Wakili, wanda wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi garkuwa da shi ranar Juma’a.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Filato, DSP Alfred Alabo, a wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Juma’a, ya bayyana cewa jami’an rundunar sun kama wadanda suka sace basaraken.
A cewarsa: “An samu kiran tashin hankali daga hedikwatar ‘yan sanda ta Angware cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun shiga fadar Agwom Izere da karfi, suka yi garkuwa da shi. Nan take jami’an ‘yan sanda karkashin jagorancin DPO na Angware, SP Timothy Bebissa, suka garzaya wurin da lamarin ya faru domin ceto sarkin, amma ‘yan bindigar sun yi artabu da bindiga, inda masu garkuwan suka harbe wani mai gadin farar hula da ba a tantance ba. kuma daya daga cikin ‘yan sandan ya samu rauni a harbin bindiga.”
Ya ce ’yan sanda da sauran jami’an tsaro da kungiyoyin sa kai sun yi dabara, inda suka dauki matakin ceto basaraken.
“An kuma kama wasu mutane biyu da ake zargi [da alaka da] wannan mugunyar,” in ji shi.
DSP Alabo ya ci gaba da cewa an kai jami’in da ya raunata asibiti yayin da aka ajiye gawar mai gadin farar hula a asibitin domin a tantance gawarwakin, yana mai jaddada cewa har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike domin kamo sauran ‘yan kungiyar da suka tsere.