Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce irin barnar da aka yi sakamakon mamayar Rasha a Ukraine ta wuce duk wani tunani da ake dashi.
A cikin wata sanarwa d ata fitar saboda cika kwana dari da fara yakin Ukraine, babban daraktan kungiyar Robert Mardini, ya ce zai yi wuya a ce an zuzuta lamarin musamman, wajen fadan yawan fararen hular da aka kashe ko aka jikkata.
Ya ce an yi asarar rayuka, sannan an dai daita iyalai, an lalata gidaje da makarantu da ma asibitoci.
Irin asarar da aka tafka a Ukraine babu dadin ji balle gani, ‘yan kasar miliyan 14 sun bar gidajensu, sannan toshe tashar ruwan black sea ta hana Ukraine fitar da hatsinta.
Tuni Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa rikicin wanda ya ya raba miliyoyin mutane da muhallansu za a jima ana yinsa. In ji BBC.