Hukumar hana yaɗuwar cututtuka ta kasa NCDC, ta buɗe cibiyar bayar da agajin gaggawa yayin da adadin waɗanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar kwalara ya kai 53 a fadin ƙasar.
A cewar sanarwar da hukumar ta NCDC ta fitar a ranar Litinin din da ta gabata kan dandalinta na, wani bincike da aka yi kan hadarin kamuwa da cutar ya nuna akwai matukar hadarin kamuwa da cutar sosai, dalilin da ya saka aka buɗe cibiyar bayar da da agajin gaggawa ta ƙasa EOC.
“Ya zuwa ranar 24 ga Yuni, 2024, an samu jimillar mutane 1,528 da ake zargi da kamuwa da cutar da kuma mutuwar mutum 53 a cikin jihohi 31,” in ji NCDC.
Hukumar ta kuma jaddada buƙatar a kara wayar da kan jama’a da daukar matakan kariya domin dakile yaduwar cutar.