Barcelona ta tabbatar da nadin Hansi Flick a matsayin sabon kocinta a hukumance.
Flick ya gaji Xavi bayan da kulob din ya yanke shawarar rabuwa da tsohon kyaftin din a karshen kakar wasa ta bana.
Kocin na Jamus, wanda ya yi suna wajen jagorantar Bayern Munich a gasar cin kofin zakarun Turai a kakar wasa ta 2019-20, bai da aiki tun bayan korar da aka yi masa a matsayin kocin tawagar Jamus a watan Satumba.
Yarjejeniyar shekaru biyu da Barcelona ta nuna matsayin kocin Flick na farko a wajen kasarsa.