A ranar Juma’a ne Barcelona ta sallami kocinta Xavi Hernandez.
Kulob din na Kataloniya ya bayyana hakan a wata sanarwa ta shafin yanar gizon su.
A wani bangare sanarwar ta kara da cewa: “A yau Juma’a, Shugaban FC Barcelona Joan Laporta ya sanar da Xavi Hernández cewa ba zai ci gaba da zama kocin kungiyar farko a kakar wasa ta 2024-25 ba.
“FC Barcelona na son gode wa Xavi saboda aikin da ya yi a matsayin koci, da kuma yadda ya taka rawar gani a matsayinsa na dan wasa da kuma kyaftin din kungiyar, tare da yi masa fatan samun nasara a nan gaba a duniya.
“Xavi Hernández zai horar da kungiyar a karo na karshe a wasan da za su yi waje da Sevilla ranar Lahadi.”