Barcelona ta saɗa tsohon ɗan wasan tsakiyarta Deco a matsayin sabon daraktan wasannin ƙungiyar
Dan kasar Portugal, haifaffen Brazil, mai shekara 45, ya sanya hannu kan kwantiragin shekara uku a Nou Camp.
A shekarar 2004 ne Deco ya fara komawa Barcelona daga Porto, kuma ya lashe gasar La Liga sau biyu a kakar wasanni huɗu, da kuma gasar Zakarun Turai a shekarar 2006.
Barca ta ce Deco zai jagoranci sabuwar aƙidar wasansu kuma zai yi aiki tare da kociyan ƙungiyar Xavi da sauran masu taimaka masa.
Ƙungiyar ta ce tana shirin yi wa bangaren gudarwarta garambawul, inda ba da cikakkun bayanai nan da makonni masu zuwa.
Tsohon daraktan wasanni Jordi Cruyff ya bar kungiyar a watan Mayu.
Deco ya kuma buga kakar wasa biyu a Chelsea bayan zamansa a Sifaniya kafin ya koma Brazil inda ya yi ritaya a kungiyar Fluminense da ke Rio de Janeiro.