Manchester City da Barcelona sun amince kan farashin Bernardo Silva, wanda zai iya ba da damar Frenkie de Jong ya bar Camp Nou a bazara.
A cewar Gerard Romero, Barcelona da Man City sun cimma yarjejeniya ta kasa da fam miliyan 67, bayan da koci Pep Guardiola ya ki amincewa da barin Silva a ‘yan makonnin nan.
Babu shakka ci gaban zai amfanar da Chelsea da Manchester United, bayan an danganta su da De Jong a wannan bazarar.
Rahotanni sun bayyana cewa, mai kungiyar Chelsea Todd Boehly ya tattauna da De Jon ta wayar tarho, duk da cewa dan wasan tsakiyar dan kasar Holland ya nanata sha’awarsa ta ci gaba da zama a Catalonia.
Ita kuwa Man United tana son sayen De Jong, wanda ya yi aiki tare da kocinsu Erik ten Hag a lokacin da suke Ajax.