Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya kammala shirin gyara da inganta tsarin ginin filin wasa na Jami’ar Bayero Kano (BUK), domin karɓar wasannin gasar kwallon kafa ta ƙasa da sauran manyan wasanni.
Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan da Barau FC, ƙungiyar kwallon kafa da Sanata Barau ya kafa, ta samu nasarar hawa daga Nigeria National League (NNL) zuwa Nigeria Premier Football League (NPFL). Wata tawaga daga ofishin Sanatan, wacce ta haɗa da Shugaban Ma’aikata, Farfesa Muhammad Ibn Abdallah; Mai Bada Shawara na Musamman kan Harkokin Yada Labarai, Alhaji Ismail Mudashir; da Mai Bada Shawara na Musamman kan Matasa da Wasanni, Kwamared Kabiru Ado Lakwaya, ta kai ziyara ga shugabancin jami’ar karkashin jagorancin Shugaban Jami’ar, Farfesa Haruna Musa, a ranar Talata.
Farfesa Abdallah, wanda ya jagoranci tawagar, ya bayyana cewa Sanatan ya ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da cewa BUK na da filin wasa na zamani da zai amfani jami’ar, al’ummarta, da kuma matasa masu sha’awar kwallon kafa. Da yake mayar da martani, Farfesa Musa ya gode wa Sanatan bisa wannan kyakkyawar manufa, yana mai cewa hakan ya yi daidai da tsare-tsaren da ya gabatar wa Majalisar Gudanarwa ta jami’ar lokacin da yake neman mukamin shugaban jami’ar. Ya kara da cewa jami’ar a shirye take ta ba da dukkan goyon baya don ganin an aiwatar da wannan aikin cikin nasara.