Sanata Barau Jibrin mai wakiltar Kano ta Arewa, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Kano a shekarar 2023 a ranar Lahadi a Kano.
Barau Jibrin, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan kasafin kudi, ya kuma nada tare da kaddamar da tsohon gwamnan jihar, Hafiz Abubakar a matsayin daraktan yakin neman zabensa, kuma shugaban kwamitin yakin neman zabe.
Hafiz Abubakar ya jagoranci wani kwamiti mai mutum 17 da aka zabo daga gundumomin Sanatoci uku da kuma kwamitin mutum 27 da aka zabo daga kananan hukumomin jihar 44, domin sa ido kan yakin neman zaben.
Dan takarar gwamnan ya bukaci kwamitocin su yi aiki kafada da kafada da daraktan yakin neman zaben, domin samun nasara a zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC.
A jawabinsa na karbar, Farfesa Hafiz Abubakar ya ce, kwamitin zai kaddamar da kananan kwamitoci a shafukan sada zumunta, kungiyoyin dalibai da kuma ‘yan kasuwa da za su gudanar da yakin neman zaben.
“Za mu fitar da dabarun tunkarar kamfen na Barau Jibrin wanda zai shafi al’umma, ‘yan kasuwa, shugabannin addini da kungiyoyi. In ji Farfesa Hafiz.