Barau ya samu rakiyar Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane, Yusuf Abdullahi Ata, Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Abubakar Bichi, da sauran manyan jiga-jigan APC.
Gangamin ya tara dubban jama’a da magoya bayan APC, inda shugabannin jam’iyya suka roki mazauna yankin da su fito kwansu da kwarkwata domin su dangwalawa APC.
A jawabinsa, Sanata Barau Jibrin ya ce zaben dan takarar APC, Ahmad Kadamu, zai ƙara tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta ci gaba da aiwatar da ayyuka a yankin.
“Ku fito ku kada wa APC kuri’unku a zaben cike gurbi, hakan zai zama farkon nasarorin da za mu samu a zaben gwamna da shugaban kasa mai zuwa a 2027.”
Bayan gangamin kamfen, jerin gwanon motocin yakin neman zaben ya wuce zuwa Ghari, inda aka mika tutar jam’iyyar APC ga dan takarar zaben ƙarishe na kujerar.