Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta sanar da naɗa Ladan Bosso a matsayin sabon kocinta kafin fara kakar wasa ta bana.
Wata sanarwa da kulbo ɗin ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ta ce nan gaba zai yi ƙarin bayani kan yarjejeniyar da ya ƙulla da Boso.
Wannan ne karon farko da ƙungiyar ta jihar Kano za ta buga babbar gasar firimiya ta Najeriya NPFL bayan samun gurbi a kakar wasa ta 2024-25 a gasar NNL.
Ladan Bosso ya jagoranci tawagar Najeriya ta ‘yan ƙasa da shekara 20 wato Flying Eagles zuwa kofin ƙasashen Afrka da kuma Kofin Duniya daga 2020 zuwa 2023.
Haka nan ya yi aikin horar da ƙungiyoyi a Najeriya da suka haɗa da Bayelsa United da kuma El-kanemi Warriors.