Gwamnan Kano, Kabiru Abba Yusuf, ya umarci akanta janar na jihar da ya rufe asusun bankuna na dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnati ba tare da ɓata lokaci ba.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa gwamnan ya bayar da umarnin ne yayin wata ganawa da yake yi da shugaban hukumar tattara haraji na jihar ta kano da dukkan shugabannin hukumomi da ma’aikatun gwamnatin jihar a gidan gwamnati.
Abba Kabir Yusuf ya ce ya dauki matakin ne domin tabbatar da cewa dukkannin kuɗaɗen shigar gwamnati na shiga asusun gwamnati guda ɗaya zuwa lalitar hukuma ta yadda za a yi amfani da su ta hanyar da ta dace.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan ya tura buƙata majalisar dokokin jihar yana neman su sahale masa yin ƙwarya-ƙwaryar kasafi na fiye da naira biliyan 99, ƙari a kan kasafin.