fidelitybank

Bankuna na karkatar da sababbin kudade – Bankin Micro

Date:

Manajan Darakta na Bankin Micro Finance na Yobe ,Sheriff Muhammad Almuhajir, ya yi zargin cewa an karkatar da kudaden da babban bankin Najeriya CBN ya raba wa bankunan jihar da suka kai Naira biliyan 4.3.

MD ya yi wannan zargin ne a cikin wani hoton bidiyo na dakika 4:31 da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata.

“Ina so in fada muku cewa, na samu tabbataccen labari cewa babban bankin Najeriya reshen Damaturu ya raba wa bankunan jihar Yobe zunzurutun kudi har naira biliyan 4.3.

Karanta Wannan: IMF ya roki CBN ya sakarwa ‘yan Najeriya mara

“Kuma sama da Naira miliyan 700 na kudin an yi wa jami’an P.O.S ne,” inji shi.

Almuhajir ya kuma yi zargin cewa Naira biliyan 4.3 da aka rabawa bankunan kasuwanci ba sa yaduwa a jihar, don haka ya zargi wasu manajojin bankin da karkatar da kudaden daga jihar.

“Amma tambayar da nake son yi anan ita ce, ina wannan kuɗaɗen?”, ya tambaya.

Ya yi zargin cewa sabbin takardun Naira da ake yawowa a fadin jihar ba su kai Naira biliyan daya ba.

MD na bankin ya bayar da hujjar cewa ko da ATMs za su rika ba da tsabar kudi a kowane minti daya, ba za a iya fitar da adadin a cikin mako guda ba.

“Nawa ne yawan al’ummar jihar Yobe?

“Bankunan kasuwanci nawa muke da su a jihar nan? ATM nawa muke da shi?” Ya tambaya.

Ya kara da cewa, jihar Yobe ba ta da injinan Automated Teller Machines, (ATMs) har guda 50, domin mutane su ciri N4.3. biliyan a cikin kankanin lokaci.

Almuhajir ya kuma bayar da hujjar cewa wasu ma’aikatan Points of Sale suna samar da ayyuka masu kyau fiye da yawancin bankunan kasuwanci da ke aiki a jihar.

vanguard news nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp