Bankin Duniya ya amince da tallafin kuɗi na sama da dala biliyan biyu ga ƙasashen Gabashi da Kudancin Afirka, don taimaka musu wajen bunƙasa wadatar abinci.
A cikin wata sanarwa da bankin ya fitar, ya ce kimanin mutum miliyan 68 a yankin ke fuskantar matsalar ƙarancin abinci da barazanar yunwa.
Ya ƙara da cewa matsalolin sauyin yanayi da tabarbarewar tattalin arziki da siyasa da rikice-rikice na kara ƙamari.
Yaƙin Ukraine ya ƙara haifar da matsalar ƙarancin abinci a fadin duniya.
Bankin Duniya ya bayyana Habasha da Madagascar da suka daɗe suna fama da fari, a matsayin kasashen da za su karbi kason farko na tallafin. In ji BBC.