Bankin Duniya ya amince da kasafin kuɗi dala miliyan 300, domin gudanar da wasu ayyukan da ya ce zai inganta rayuwar ƴangudun hijira a Arewacin Najeriya.
A wata sanarwa da jaridar Daily Trust ta ruwaito, bankin ya ce a shirin mai suna Solutions for the Internally Displaced and Host Communities Project wato SOLID, wanda aka amince da shi a ranar 7 ga Agusta, za a lalubo hanyoyin da za a bi wajen taimakon ƴangudun hijira, da ma garuruwan da suke rayuwa a ciki.
Bankin ya ce rikice-rikice da suka daɗe suna addabar yankin sun raba sama da mutum miliyan 3.5 da muhallinsu, lamarin da ya shafi ababen more rayuwa, wanda a cewar bankin hakan ya sa ababen more rayuwan suka yi ƙaranci a garuruwan da suke zama.
“Daga cikin ɓangarorin da za mu mayar da hankali akwai rage illolin sauyin yanayi, samar da haɗin kai ta hanyar sasanci, tallafa wa iyalai da inganta ababen more rayuwa.”
“Muna matuƙar farin ƙaddamar da wannan aikin domin taimakon Najeriya wajen magance matsalolin da ƙasar ke fuskanta,” in ji Mathew Verghis, daraktan Bankin Duniya a Najeriya.